Suka ce suna son daina zubar da jini,don haka yana da matukar muhimmanci su samu sakon fatan yin sulhu daga bangarorin biyu,inji kakakin babbar kungiyar 'yan adawa da gwamnatin kasar Khaled Saleh a wani taron manema labarai bayan taron su a rana ta biyu.
Yayi bayanin cewa suna fatan lokacin da za su shiga wannan babban taro na tattauna matsalar kasar ya kasance za'a daina zubar da jini,don haka in ji shi akwai matukar bukatar samun tabbaci game da hakan da kuma bayanai dalla dalla sannan babban abin da ake so shi ne takardar gayyata daga MDD kafin su tsaida shawarar ko za su iya halartar wannan babban taro karo na biyu.
A wani labarin kuma Khaled Saleh yayi zargin Sojojin gwamnartin Sham da amfani da makamai masu guba a cikin garin Adra gabannin wannan taro na Geneva,abin da ya hallaka mutane 5 sannan guda 50 suka ji rauni.(Fatimah Jibril)