Wannan jami'i ya yi jawabi ta kafofin watsa labaru a wannan rana a Kampala, babban birnin kasar Uganda, cewar muhimman ayyukan da wannan hukumar zata kula da shi sun yi kama da wadanda hukumar da abin ya shafa ta kasar Kenya ke yi, wato ban da amsa tambayoyi da sauraron shawarwarin da masu yawon shakatawa sukan bayar, za ta daidaita laifuffukan da masu yawon shakatawa suka aikata. Amma bai fayyace lokacin kafuwar wannan hukumar ba.
A waje daya kuma jami'in ya nuna cewa, dakarun da ke adawa da gwamnatin kasar Somaliya wato Kungiyar matasa ta Islama, wadda ke da alaka da kungiyar al-Qaeda, tana shirin kai farmakin ta'addanci a kasar Uganda kamar yadda ta yi a birnin Kampala a ran 11 ga watan Yuli na bara, domin yin ramuwar gayya ga wadanda suka haddasa mutuwar Osama Bin Laden, tsohon shugaban kungiyar al-Qaeda da manyan kusoshin kungiyar da ke gabashin Afirka.
A ran 11 ga watan Yuli na bara, an kai hare-haren ta'addanci a birnin Kampala, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 78 yayin da 89 suka jikkata. Daga bisani kungiyar matasa ta Islama ta sanar da daukar alhakin kai harin, inda ta bayyana cewa, ta yi haka ne domin yin ramuwar gayya game da batun jibge sojojin kasar Uganda a kasar Somaliya.(Kande Gao)