Yayin da Crispus Kiyonga yake ganawa da sabon jakadan kasar Sin da ke kasar Uganda Zhao Yali, ya bayyana cewa, a 'yan shekarun da suka wuce, an samu babban sakamako mai kyau daga aikin yin hadin gwiwa a tsakanin sojojin kasashen biyu, kasar Sin ta ba da taimako wajen inganta ayyukan soja na kasar Uganda, game da haka, kasar Uganda ta nuna godiya ga kasar Sin. Kuma za ta ci gaba da yin hadin gwiwa tsakanin sojojinta da na kasar Sin.
Zhao Yali ya bayyana cewa, kasar Sin tana mai da hankali sosai kan aikin bunkasa dangantakar tsakanin kasashen biyu. A 'yan shekarun da suka wuce, sojojin kasashen biyu sun kara yin mu'amala sosai, yana cike da imani cewa, bisa kokarin da bangarorin suke yi, za a kara samun kyakkyawan sakamako daga aikin hadin kai a tsakanin kasashen biyu da kuma sojojinsu.