in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shuwagabannin Afirka sun bukaci Kenya da ta mika ikon yankin Kismayo ga Somaliya
2013-08-05 11:01:52 cri

Shuwagabannin kasashen Afirka dake baiwa shirin wanzar da zaman lafiya a Somaliya tallafi karkashin tawagar AMISOM, sun amince da bukatar da aka yi, ta kasar Kenya ta maida yankin nan na Kismayo dake bakin tashar ruwan Somaliya, da kuma filin sauka da tashin jiragen dake yankin, karkashin ikon mahukuntan kasar.

Wannan bukata dai na kunshe ne cikin wata sanarwar bayan taro da aka fitar ranar Lahadi, bayan kammalar wani zama na yini guda da shuwagabannin suka gudanar. Taron wanda shuwagabannin kasashen Uganda, Kenya, da Somaliya, da firaministan kasar Habasha, tare da sauran manyan wakilan kasashe da dama suka halarta, ya yi amanar cewa, daukar wannan mataki zai taimaka wajen sassauta yanayin rashin jituwa tsakanin kasashen Kenya da Somaliya, don gane da batun ikon yankin na Kismayo.

Har ila yau, an bukaci mika daukacin harajin da ake tattarawa daga wadancan wurare biyu ga gwamnatin kasar ta Somaliya, tare da dakatar da fidda ma'adanin kwal daga yankin na Kismayo, kamar dai yadda kwamitin tsaron MDD ya tabbatar da hakan. Don gane da bukatar karin tawagar sojojin wanzar da zaman lafiya daga tsagin kungiyar AU cikin babbar tawagar rundunar AMISOM kuwa, kasashen Kenya, da Djibouti da Saliyo, sun amince da tura karin sojoji zuwa Somaliyan. Bugu da kari kasar Somaliya ta dada jaddada aniyarta, ta gudanar da babban zaben kasa a shekarar 2016 mai zuwa.

Sai dai yayin da wadannan shuwagabanni ke bayyana daukar matakan warware takaddamar daka iya gurgunta dangantaka tsakanin Kenya da makwafciyarta Somaliya, a hannu guda ministar harkokin wajen kasar Kenya Amina Jibril Mohamed, ta bayyana cewa, zargin da ake wa kasarta don gane da irin rawar da take takawa a yankin na Kismayo ba shi da tushe bare makama, tana mai cewa, kamata ya yi, mahukuntan Somaliya su mai da hankali ga warware matsalolin rashin zaman lafiya da ke addabar kasar. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China