in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ICC ta daga shari'ar Kenyatta zuwa watan Nuwamban shekarar nan
2013-06-21 11:14:30 cri

A ranar Alhamis, kotun hukunta manyan laifuffukan yaki ta duniya (ICC) dake Hague ta daga fara shari'ar shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta zuwa ranar 12 ga watan Nuwamban 2013.

An dai sa ranar 9 ga watan Yuli a matsayin ranar da za'a fara shari'ar, to amma, tun cikin watan Aprilu, masu shari'ar suka ba da damar ba da karin lokaci ga masu kare kansu domin su samu yin shiri kan shari'ar saboda jinkirin da aka samu daga masu gabatar da masu laifin kan batun baiyyana shaida.

Ana tuhumar Kenyatta a matsayin wanda yake da hannu, amma ba kai tsaye ba, da laifuffuka biyar na cin zarafin bil adama, da suka hada da kisan gilla, tisa keya ko sauya wuri na karfi da yaji, fyade, cin zarafi da dai sauran munanan laifuka da aka aikata a lokacin tashin hankali da ya barke, bayan zaben kasar Kenya a shekarar 2007 da ta 2008, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 1000.

A cikin watan Maris na wannan shekara, aka zabi Kenyatta a matsayin shugaban kasar Kenya, kana mataimakin shugaban kasar William Ruto, shi ma ana shirin yin shari'a kansa a kotun ta Hague kan wadannan zargi, daga ranar 10 ga watan Satumban bana.

A ranar Talata da ta wuce, kotun ta ICC ta amince da bukata da Ruto ya gabatar na cewa, ba lallai ne ya kasance a kotu ba, zai kasance a kotun ne kadai idan za'a yi muhimmin zama. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China