in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ruwanda ta dare kujerar shugabancin kwamitin tsaron MDD na karba-karba a watan Aprilu
2013-04-02 10:05:53 cri
A ranar Litinin din nan Ruwanda ta haye kujerar shugabancin kwamitin tsaron MDD na watan Aprilu.

Wakilin din-din-din na kasar Ruwanda a MDD Eugene-Richard Gasana ya karbi ragamar shugabancin ne daga Vitaly Churkin, jakadan kasar Rasha a MDD wanda shi ne shugaban kwamitin na watan Maris.

Kasar Ruwanda ta shiga kwamitin tsaron MDD ne ran 1 ga watan Janairun 2013 a matsayin mamba wacce ba ta din-din-din ba, na tsawon shekaru biyu inda wa'adin zai kare a watan disamban 2014.

Ta yi aiki a baya a wannan kwamiti cikin shekarun 1994-1995, lokacin da kasar ta fuskanci kisan gillar kabilanci inda aka hallaka mutane sama da miliyan daya. (Lami Ali)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China