Kamar dai yadda kwamandan rundunar yankin Joseph Ole Tito ya bayyana wa manema labaru a jiya Litinin, tarzomar ta biyo bayan zanga-zangar nuna amincewa da hukuncin nan na tabbatar da sahihancin zaben shugaban kasar, da kotun kolin kasar ta yanke a ranar Asabar din da ta gabata.
Bayan bayyana hukunci don gane da karar kin amincewa da sakamakon zaben da firaministan Raila Odinga ya shigar gaban kotun ne dai, wadanda ake zargin suka shiga ta da hankulan jama'a a birnin na Kisumu, birni na uku mafi girma a kasar ta Kenya, lamarin da ya sanya rundunar cafke wadanda ake zargin da hannu a lamarin, tare da alkawarin gurfanar da su gaban kotu a ranar Talatar nan, da zarar 'yan sandan sun kammala binkicen da suke yi.
A cewar Tito, rundunar na zargin mutanen da ake tsare da su, da aikata laifukan da suka hada da fashi da makami, da ta da husuma, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane 2, yayin da kuma wasu 11 suka jikkata. Har ila yau, jami'in rundunar 'yan sandan ya ce, yawan mutanen da suka bar gidajensu sakamakon hakan ya kai 59, ciki had da mata 16, da maza 21 da kuma yara kanana 22. Koda yake dai ya ce yankin unguwannin talakawa dake makin gulbin birnin na Kisumu, inda rikicin ya fi kamari, a yanzu haka na karkashin kulawar jami'an tsaro. (Saminu)