Wani harin da aka kai kan sansanin al'ummun da suka guje wa gidajensu sakamakon fadace-fadacen dake aukuwa a gundumar Mandera dake arewacin Kenya, ya haddasa rasuwar mutane 15, da suka hada da yara kanana 4, tare da jikkata wasu da dama, ciki hadda wani jami'in 'yan sanda, lamarin da ya sanya shiga halin dar dar, sakamakon harin ramuwar gayya da ake hasashen aukuwarsa.
Da yake tabbatar da aukuwar wannan lamari, kwamishinan 'yan sandan yankin Banisa Samuel Mwati, ya ce, wani gurneti da aka harba ne ya haddasa wannan ta'adi, lokacin da ake tsaka da gudanar da wani taron tattaunawa domin sake farfado da yanayin zaman lafiya a sansanin. Ana dai danganta faruwar wannan balahira ne da rigingimun dake wanzuwa tsakanin al'ummomin gundumar Mandera da na Wajir, wadanda ba su ga maciji da juna.
Tuni dai, babban sifeton 'yan sanda David Kimaiyo ya bayyana cewa, ana zaton maharan sun yi nufin hallaka kwamishina mai lura da wannan yanki ne, ko da yake dai hakan su bai-cimma-ruwa ba. Har ila yau Kimaiyo ya tabbatar da daukar matakan tura karin jami'an tsaro zuwa yankin da wannan lamari ya auku, domin dai kaucewa kara tabarbarewar lamura.
Dauki-ba-dadi tsakanin al'ummun Garre da na Degodia a wannan yanki na Mandera dai na kara tsananta ne, tun bayan da al'ummar Degodia suka samu nasarar amshe kujerar wakilcin masarautar yankin na Mandera daga tsagin al'ummmar Garre, yayin babban zaben shekarar 2007 da ya gabata. (Saminu)