An dai gudanar da sanya hannu kan wannan batu ne a birnin Nairobi, gaban manyan jagororin jam'iyyun, da gwamnonin kasar, da kuma zababbun 'yan majalisun dokokin kasar, da kuma wakilan mata zababbu.
Cikin wadanda suka amince da wannan shiri na dunkulewa da aiki tare, bayan kammalar babban zaben kasar, akwai mataimakin Firaminista Musalia Mudavidi, wanda shi ne ya zo na uku a yawan kuri'un da aka kada yayin zaben daya gabata. Sai kuma mai shari'a Eugene Wamalwa, da kuma ministan ma'aikatar makamashi Kiraitu Murungi.
Da yake jawabi yayin bikin rattaba hannun, shugaba Kenyata ya ce, gwamnatinsa za ta martaba doka da oda, za kuma ta karbi sakamakon da kotu za ta yanke, don gane da karar da tsagin wasu 'yan adawa suka gabatar, dake kalubalantar sahihancin sakamakon zaben da ya bashi nasara. Daga nan sai sabon shugaban kasar ta Kenya ya nanata aniyar gwamnatinsa, na yin cudanya da dukkanin jagororin al'umma, da ragowar masu ruwa da tsaki, domin tabbatar da daukaka matsayin kasar zuwa mataki na gaba, yana mai alkawarin cewa, babu wani bangare na kasar, ko wata al'umma da za a mayar saniyar ware.(Saminu)