in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cibiyar kididiga da bincike ta Fich ta sanar da matsayin bunkasar hada-hadar kudi da kasuwanci tsakanin Afirka da Sin
2011-12-29 14:23:42 cri
Kasuwanci tsakanin Afirka da Sin ya kasance wani abu mai muhimmanci a cikin tarihi, da kuma ke bunkasa yankin Afirka na kudu da sahara. Cibiyar kididiga da bincike ta Fitch Ratings ita ce ta sanar da hakan a cikin wani sakamakon bincike da ta gabatar a ranar Laraba.

Cibiyar ta sanar da cewa, alamu sun nuna cewa, kasuwanci tsakanin Afirka da Sin zai kara bunkasa a nan gaba. A halin yanzu Sin ta kasance mai babban matsayi na 2 da Afirka ke sayen hajojin ta, kuma babban dandalin kasuwanci na 3 a duniya bayan Turai da Amurka.

Kamar yadda binciken cibiyar ya sanar, Afirka ba ta kasance ba kawai mai shigowa da kaya daga Sin, ta kasance wani fage da kasar Sin ke zuba jari cikin shi a waje.

Rashin sa dabaibayar siyasa irin yadda gwamnatocin kasashen yamma ke yi, kamar mulki, da kaidojin mahali tare da kaidojin gwagwarmaya sun sa Sin ta kasance dausayi mai jawo hankalin jama'a da kuma bashi da tsada ga kasashen Afirka kamar yadda cibiyar kididiga ta Fitch ta bayyana.

Hulda ta fannin kudi da kasuwanci da Sin ta kasance wani babban abu mai muhimmanci da zai iya cika gibin kayen more rayua a Afirka cewar cibiyyar binciken. Ta kara da cewa, idan ake yi amfani da ma'adinai kamar yadda ya kamata, Sin za ta taimakama Afirka ta bunkasa da sauri. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China