in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta taya kasar Kenya murnar gudanar da babban zabe cikin lumana
2013-03-11 16:33:24 cri

Yau Litinin ranar 11 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta nuna a nan birnin Beijing cewa, Sin na taya Mr. Uhuru Kenyatta murnar lashe zaben shugaban kasar ta Kenya, tare da yaba yadda aka gudanar da zaben cikin lumana.

An ba da labarin cewa, kwamitin zabe na kasar Kenya ya gabatar da sakamakon babban zaben a ran 9 ga wata, wanda ya nuna cewa, mataimakin firaministan kasar Uhuru Kenyatta ya lashe zabe.

Hua Chunying ta ce, Sin da kasar Kenya na da danko zumunci. Kuma kasar Sin tana mai da hankali sosai, kan dangantakar dake tsakaninta da kasar Kenya, tare da mai da kasar Kenya matsayin muhimmiyar kawa a Afrika dangane da hadin gwiwa. Sin a cewar kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar, na fatan kara hadin kai da sabuwar gwamnatin Kenya, tare da kara bunkasa dangantakar dake tsakaninsu, da bunkasa cin gajiyar jama'ar kasashen biyu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China