Hukumar zabe ta kasar Zimbabwe ta sanar a ran 3 ga wata cewa, shugaba mai ci Rober Mugabe ya lashe zabe da aka yi a ran 31 ga watan Yuli. Shugaban kasar Nijeriya Goodluck Jonathan ya yi maraba da sakamakon zabe, kana ya taya Robert Mugabe murnar ci gaba da mulki.
A cikin wata sanarwar da mai ba da shawara na musamman ga shugaban kasar Nijeriya kan harkokin yada labarai da fadakarwa ya bayar, Goodluck Jonathan ya kalubalanci shugaba Robert Mugabe da jam'iyyarsa ta ZANU-PF da su dukufa kan tabbatar da zaman alheri tsakanin jama'a da samun bunkasuwar kasar.
A cikin sanarwar, Goodluck Jonathan ya yi kira ga Robert Mugabe da ya tabbatar da cewa duk wani mutum ko jam'iyya wanda bai yarda da sakamakon zaben ba, da su bayyana burinsu ta hanyar da ta dace. A sa'i daya kuma, yana fatan shugaban babbar jam'iyya mai adawa, Morgan Tsvangirai da ya dauki mataki da ya dace domin bayyana korafinsa, saboda duk wani mataki da ba bisa doka ba, zai iya haifar da rikicin siyasa a kasar. (Amina)