Da sanyin safiyar Larabar nan 31 ga wata ne dubun dubatar al'ummar kasar Zimbabwe suka fara kada kuri'unsu a babban zaben kasar da zai fidda sabon shugaban kasar, da 'yan majalissun dokoki, da kuma 'yan majalissun zartaswar kananan hukumomi.
Tuni dai aka yi hasashen fafatawa mai tsanani tsakanin shugaban kasar mai ci Robert Mugabe, da tsohon dan hamayyarsa kuma firaministan kasar Morgan Tsvangirai.
Bisa kididdigar da aka yi, kimanin mutane miliyan 6.4 ne za su jefa kuri'unsu, domin zaben 'yan majalisun dokokin kasar sama da 200, da kuma dubban 'yan majalissar zartaswar kananan hukumomin kasar.(Saminu)