A ranar Laraba hukumar zabe ta kasar Zimbabwe ZEC ta bayyana cewa, an kamala zabe lami lafiya kuma ba tare da magudi ba, inda ma har an fara kirga kuri'un. Shugabar Hukumar zaben Rita Makarau yayin taron manema labarai da aka shirya bayan an kamala zaben, ta ci gaba da cewa ta tabbata an gudanar da zaben ba tare da magudi ba bisa rahotanni da ta samu daga jami'an hukumar.
Mutane kusan miliyan 6.4 wato kusan rabin adadin yawan 'yan kasar ne aka yiwa rajistar zabe a cibiyoyin zabe sama da dubu 9, domin su zabi wanda zai hau kujerar mulkin kasar na tsawon shekarau biyar, tsakanin shugaban kasar da ya dade kan kujera kuma mai shekaru 89, Robert Mugabe da tsohon abokin hamayarsa kuma praministan kasar Morgan Tsvangirai.
Makarau ta kara da cewa, a yau Alhamis ne za'a fara tantance adadin kuri'un.
A halin da ake ciki, an riga an fara kirga kuri'u a wurare da aka kamala jefa kuri'a. Hukumar zaben ta ce nan da kwanaki biyar ne za'a iya sa ran samun sakamakon zaben.
Shugaban tawagar sa ido ta kungiyar hada kan kasashen Afirka AU, kuma tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa an yi zaben cikin zaman lafiya, walwala, adalci kuma bisa tsari. (Lami)