Da yake jawabi ga taron kungiyar kanana hukumomin kasar Zimbabwe a karo na 3 a garin Mutare mai nisan kilomita 270 gabas da Harare, babban birnin kasar, wanda a kan shirya a ko wadanne shekaru 2, shugaba Mugabe ya ce, Chinamasa bai bayyana masa ra'ayinsa dangane da batun ba, wanda shi ne ke dauke da nauyin wannan aiki a yanzu.
Kafin Chinamasa, ministan harkokin tsarin mulkin kasa da majalisa na Zimbabwe Eric Matinenga shi ne ya jagoranci aikin tsarin mulkin kasa har zuwa lokacin da aka rubuta daftarin, wato bayan da aka gabatar da kuri'ar raba gardama a watan Maris.
Shugabannin kasar Zimbabwe sun amince da cewa, wajibi a samar da sabon kundin tsarin mulkin kasa kafin a gudanar da zabe.
Matinenga ne ya gabatar da daftarin tsarin mulkin kasa ga majalisar dokokin kasar a ranar Talatar da ta gabata, kana 'yan majalisar suka amince da ita a ranar Alhamis. A halin yanzu daftarin na jiran nazarin majalisar dattijan kasar a ranar Talata, inda daga bisani shugaba Mugabe zai ba da amincewarsa domin ta zamo sabuwar doka ta kasar.
To amma kuma shugaba Mugabe ya ce, ko da 'yan majalisar dattijan sun ba da amincewarsu kan sabon daftarin tsarin mulkin kasa, sai masana harkokin shari'a za su tabbatar da ingancinta. (Lami Ali)