Rahotanni daga kafofi daban-daban na nuna cewa jami'yyar Africa National Union Patriotic Front (Zanu-PF) ta cimma nasara.
Kamfanin dillancin labaran kasar New Ziana ya bada rahoto ranar alhamis cewa wani jami'in jam'iyyar wanda ba'a fadi sunansa ba ya yi ikirarin cewa sun yi nasarar lashe kujerar shugaban kasa da kujerun majalisar dokoki, inda yake cewa sun murkushe jam'iyyar MDC-T.
Babban mai hamaya da shugaba Mugabe a siyasa tun shekarar 1997, Tsvangirai, yayi korafi ranar alhamis cewa an tafka magudi a zaben inda ya ce sakamakon ko kadan bai nuna burin jama'a ba.
Tsvangirai ya ci gaba da cewa an tabka magudi a zaben saboda an karya wasu muhimman dokoki wadanda zasu shafi yadda sakamakon zaben zai kasance.
Wani na hannun daman Mr Tsvangirai ya baiyanawa kamfanin dillancin labaran kasar Sin, Xinhua cewa abubuwa ba su yi wa firaministan kyau ba. Kalaman firaministan ba su samu goyon bayan masu sa ido kan zaben daga nahiyar Afirka ba, wadanda sune suka fi yawa cikin masu duba zaben da aka yi ran 31 ga watan Yuli, wadanda yawansu ya kai 1500.
A halin da ake ciki, jam'iyyar shugaba Mugabe ta lashe 26 cikin kujeru 28 na 'yan majalisa a zaben kamar yadda hukumar zaben ta sanar a daren ranar alhamis.
Hukumar zabe ta kasar Zimbabwe ta bada sanarwar sakamakon zaben kujerun majalisa na yankuna uku, a rukunin farko. (Lami Ali Mohammed)