Sanarwar ta ce, Ban Ki-moon ya sa lura sosai kan babban zaben kasar Zimbabwe, da nuna yabo ga jama'ar kasar da su jefa kuri'u cikin lumana. Kana yana fatan jama'ar kasar Zimbabwe za su ci gaba da kwantar da hankalinsu yayin da ake kidaya kuri'u har zuwa lokacin kammala zaben. Kuma Ban Ki-moon ya yi kira ga shugaba, firaministan kasar na yanzu da jam'iyyu daban daban na kasar da su tabbatar da cika alkawarinsu na gudanar da zaben cikin lumana, da kira ga masu goyon bayansu da su kiyaye kwanciyar hankali.
Sanarwar ta kara da cewa, MDD tana son shugabannin kasar Zimbabwe za su kiyaye nauyi dake kansu da gudanar da ayyukan siyasa, kana su zama masu la'akari da ra'ayoyin bangarori daban daban, ci gaba da aiwatar da manufofin gudanar da ayyuka ta hanyar demokuradiyya da yin kwaskwarima, da kuma sa kaimi ga farfado da tattalin arzikin kasar don amfanin dukkan jama'ar kasar. (Zainab)