A jiya Lahadi 2 ga wata a kasar Japan, shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe mai shekaru 89 a duniya ya nuna cewa, ba zai sauka daga mukaminsa ba, duk da matsin lambar da kasar Birtaniya da dai sauransu suke yi masa. Za a gudanar da babban zaben kasar Zimbabwe a wannan shekara, kuma zai ci gaba da mulkinsa, muddin ya lashe zaben.
Yayin da ya halarci taron raya nahiyar Afrika karo na biyar a kasar Japan, Robert Mugabe ya shedawa manema labarai cewa, yana tunanin yin murabus, amma ko zai sauka daga mukaminsa ko a'a ba abin da ya shafi kasar Birtaniya ba ne, jama'ar kasarsa ne ke da hakkin yanke shawara.
A watan Maris na bana, an samu nasarar jefa kuri'ar jin ra'ayin jama'a kan sabon kundin tsarin mulkin kasar, inda EU ta soke wasu takunkumin da ta garkamawa kasar, amma Robert Mugabe da matarsa da wasu manyan jami'an kasar ciki hadda ministan tsaron kasar har yanzu suna cikin takardar sunayen wadanda aka saka ma takunkumi.
Kwanan baya, Robert Mugabe ya kaddamar da sabon tsarin mulkin. Bisa tanade-tanade dake cikinsa, wa'adin aikin shugaban kasar ya kai shekaru biyar, kuma yana iya ci gaba da mulki sau daya bayan kasancewar wa'adin farko. Don haka, Robert Mugabe mai shekaru 89 zai samu damar ci gaba da mulkinsa, idan ya lashe zaben da za a yi cikin wannan shekara. (Amina)