Mugabe dan shekaru 89 a duniya,ya sheda ma duban magoya bayansa da suka taru a filin wasa dake Harare babban birnin kasar cewa zai tabbatar da cewa bakaken fata 'yan asalin kasar ne kawai zasu mallaki dukiyar kasar koda kuwa zasu hada gwiwa da kamfanonin kasashen waje ne domin samun isassun jari.
A cewar Mista Mugabe, albarkatun kasa na jama'r kasashen ne kuma ya fi muhimmanci idan an kwatanta da jarin da kasashen waje zasu zuba. Kasar Zimbabwe wadda keda albarkatun kasa na lu'u lu'u da zinari tana kokarin farfadowa ne daga fiye da shekaru 10 da tayi tana fama da matsin tattalin arziki musamman ma bisa ci gaban da aka samu a wannan bangaren na hakar ma'adinai. (Fatimah Jibril)