Mugabe wanda ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyin manema labaru sa'o'i 24 kafin fara kada kuri'un babban zaben, ya ce yana da karfin gwiwar sake lashe zaben. Ya ce yana fatan jam'iyyarsa ta Zanu-PF za ta yi awon gaba da kaso mai rinjaye na kuri'un da za a kada, kamar dai yadda hakan ta faru a zaben kasar na farko, karkashin salo irin na dimokuradiyya a shekarar 1980. Hakan a cewarsa zai tabbatar da goyon bayan da jama'a kewa jam'iyyarsu ta 'yan kasa, sabanin jam'iyyun da aka kirkira a ketare.
Kalaman shugaba Mugabe na zuwa ne daidai lokacin da wasu manyan jami'an hukumomin tsaron kasar suka bayyana cewa, ba za su amince da sakamakon zaben ba, muddin dai mutumin da bai ba da gudummawa ga samun 'yancin kasar ne ya samu nasara. Kalaman da ake gani alamu ne, dake nuni ga yiwuwar kin amincewarsu da sakamakon, muddin dai tsohon dan adawa kuma firaministan kasar Morgan Tsvangirai ne ya lashe zaben.
Tuni dai jam'iyyar MDC-T ta Firaminista Tsvangirai's ta soki wannan furuci, tana mai cewa hakan alama ce dake nuna rundunar sojin kasar ba ta da niyyar bada damar mika mulki ga halastacciyar gwamnati da jama'ar kasar za su zaba.(Saminu)