'Yan kasar ta Zimbabwe za su yi zaben shugaban kasa ranar Laraba bayan an shafe shekaru hudu karkashin gwamnatin hadaka ta hadin gwiwa.
A yayin ganawa da manema labarai a Harare, babban birnin kasar, shugabar hukumar zabe (ZEC), Rita Makarau ta bayyana cewa an ci karfin dukkan shirye-shirye domin dukkan kayayyaki da ake bukata an gama tanadinsu.
Ta ce nan da zuwa ranar Lalata hukumar za ta kammala dukkan shiri.
Shugabar ta ce, sun yi koyi daga kurakurai da aka samu a yayin zaben musamman wanda aka gabatar makonni biyu da suka wuce, don haka an yi dukkan tanadin tabbatar da cewa za a yi zaben ba tare da wata tangarda ba.
An fuskanci matsalolin kayan aiki a yayin zaben na musamman wanda aka shirya domin jami'an 'yan sanda da sauran jam'ai da za su yi aiki a ranar zaben, inda ta kai ga da dama daga cikinsu ba su samu jefa kuri'a ba. (Lami)