Shugaban kasar Zimbabwe Robert Gabriel Mugabe da firaministan kasar Morgan Richard Tsvangirai sun yi rajista a ran 28 ga wata domin shiga zaben shugaban kasar, kuma wannan shi ne karo na uku da wadannan mutane biyu za su yi takara cikin zaben.
Robert Gabriel Mugabe da Morgan Richard Tsvangirai ta hannun wakilan jam'iyyunsu, sun mika takarda zuwa ga kotun gabatar da sunayen 'yan takara a wannan rana, ban da haka, kotun ta sami takardar ministan masana'antu da kasuwanci Welshman Ncube.
Duk da haka a ganin manazarta, Robert Gabriel Mugabe da Morgan Richard Tsvangirai ne suka kasance manyan mutane biyu da za su yi takarar mukamin shugaben kasar.
Robert Gabriel Mugabe ya sanar da gudanar da zabe a ran 31 ga watan Yuli a kwanan baya, amma ba'a sami amincewa daga wajen Morgan Richard Tsvangirai ba bisa dalilin cewa lokaci bai yi ba.
Kotun tsarin mulkin kasar za ta yanke shawara kan wannan batu a mako mai zuwa, idan kotun ta ki amince da matsayin Morgan Richard Tsvangirai, to wadannan mutane biyu za su yi yakin neman zabe na tsawon kasa da wata daya kawai.
Kafin wannan kuwa, ana bin kididdigar jin ra'ayin jama'a, inda Robert Gabriel Mugabe ya samu mafi yawan goyon baya, kana Morgan Richard Tsvangirai bai sami goyon baya sosai ba, saboda zargin abin kunya na cin hanci da karbar rashawa da kuma matsalar aure bayan ya hau kan kujerar babban jami'in kasar, har tsawon shekaru hudu. (Amina)