A kuma ranar Lahadin data gabata ne majalissar ta zartaswa ta yi zamanta na farko ba tare da wakilcin ko da mutum guda daga jam'iyyar 'yan uwa musulmi ba.
A ranar Asabar din da ta gabata, yayin da yake amsa tambayoyi cikin wani shiri da gidan talabijin din kasar ya yada, firaministan rikon kwaryar kasar ta Masar Hazem al-Beblawi, ya yi kira da a kawo karshen rarrabuwar kan dake addabar kasar a halin yanzu, yana mai cewa lokaci yayi da za a gudanar da sulhu, a kuma dinke barakar dake tsakanin al'ummar kasar. Bugu da kari Al-Beblawi ya jaddada cewa aikin gwamnatin ta wucin gadi bai wuce kafa kyakkyawan ginshiki ga zababbiyar gwamnati mai zuwa ba. (Saminu)