Jakadan na Masar ya gabatar da matsayin gwamnatin kasar dangane da mataki da kwamitin tsaro da zaman lafiya na kungiyar AU ya tsayar a ranar 5 ga watan Yuli 2013, wanda ya dakatar da kasar Masar daga kungiyar AU har sai ta dawo kan tsarin dokokin kasa.
Omar har wa yau ya nemi karin haske kan kwamitin bincike da kungiyar AU ta kafa daga bisani kan kasar Masar da kuma ayyukan da zai gabatar.
Kwamitin binciken na musamman da shugabar gudanar da kungiyar AU ta kafa dangane da hali da ake ciki a kasar Masar, ya yi zaman shawarwari na farko ran 16 ga watan Yuli a Addis Ababa.
Yayin jawabi ga 'yan jarida bayan ganawar tasu, jami'an biyu sun bayyana cewa sun yi tattaunawa kuma sun cimma matsaya.
Zuma ta ce kwamitin zai kai ziyara kasar Masar don ganawa da masu ruwa da tsaki kana zai dawo da rahoto ga kwamitin tsaro da zaman lafiya na kungiyar.(Lami)