Cikin wadanda aka nada domin gudanar da wannan muhummin aiki hadda mai baiwa shugaban kasar shawara kan kundin mulkin Ali Awad Saleh, wanda aka nada matsayin babban jami'in tsare-tsaren aikin kwamitin. Ana sa ran cewa wannan kwamiti zai fara gudanar da ayyukansa a ranar Lahadin nan, a helkwatar rusasshiyar majalissar kolin kasar.
Wannan dai mataki daya ne daga matakan da sojojin kasar suka bayyana dauka, da amincewar ragowar jam'iyyun siyasar kasar da malaman addinai, don gane da warware matsalolin kasar, biyowa bayan tsige tsohon shugaban kasar Mohammed Morsi daga mukaminsa a farkon wannan wata na Yuli. (Saminu Alhassan Usman)