in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta yi Allah wadai da juyin mulki a Masar
2013-07-06 16:05:20 cri
Gwamnatin kasar Najeriya ta yi Allah wadai da juyin mulkin soja da aka yi a kasar Masar inda ta ce wannan lamari na bakin ciki ya saba dokokin kungiyar hadin kan kasashen Afirka, wanda ya hana yin sauyin gwamnati ta hanyar da ta saba doka.

Don haka gwamnatin ke kira ga rundunar sojin ta bari a ci gaba da tsarin demokradiyya a kasar.

Da yake nuna ra'ayinsa dangane da matakin soja a cikin wata sanarwa ranar Jumma'a, ministan harkokin wajen kasar Najeriya Amabasada Olugbenga Ashiru ya baiyana cewar wannan mataki tamkar dakile burin jama'ar kasar Masar ne na baiyana zabinsu ta hanyar zabe.

Ministan na mai ci gaba da cewa, Najeriya na kiran a mayar da tsarin demokradiya a kasar Masar nan da nan, kana ta yi kira ga jama'ar kasar su zamo masu la'akari wajen nuna rashin jin dadinsu. (Lami Ali)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China