Bisa labarin da gidan telebijin na Al Jazeera ya bayar, an ce, ofishin masu gabatar da kararraki na kasar Masar ya bayar da wata sanarwa a ranar 13 ga wata, inda ya bayyana cewa, ya samu wasikar zargin Morsi, da ragowar jigajigan 'yan rajin kishin Islama 8 ciki hadda jagoran kungiyar 'yan uwa musulmi Mohamed Badie. Bisa sakamakon binciken da ake yi, akwai yiwuwar tsai da kudurin gabatar da wadannan mutane a gaban kotu.
Bisa al'ada dai, bangaren masu gabatar da kararraki ya sanar da kudurin gabatar da wadanda ake zargi gaban kotu a fili.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, bangaren masu gabatar da kararraki bai bayyana sunan wanda ya gabatar da sakon korafin ba. kamfanin dillancin labaru na Reuters ya bayar da wani labari dake nune cewa, bisa dokokin kasar ta Masar, bangaren masu gabatar da kararraki na iya fara yin bincike bisa takardar zargi da 'yan sanda ko fararen hula suka gabatar.
A kwanakin baya, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Amurka Jen Psaki ta bayyana bukatar hukumomin a kasar Masar da su saki tsohon shugaban kasar Morsi tare da dakatar da kama shugabannin kungiyar 'yan uwa musulmi. (Zainab)