Yayin bikin rantsuwar, Mohamed M.El Baradei ya yi alkawarin cewa, zai dukufa wajen kiyaye tsaron kasa, girmama tsarin mulkin kasa da dokokin kasa, kiyaye ikon mulkin kasa da cikakken yankin kasa da kuma moriyar al'ummomin kasa.
Bisa labarin da aka samu daga kamfanin dillancin labarai na Gabas ta Tsakiya, an ce, firaministan gwamnatin wucin gadin kasar Hazem el-Beblawi ya riga ya fara ayyukan kafa sabuwar gwamnatin kasar, yanzu an riga an tsai da sunayen ministoci da dama ciki har da na ministan harkokin wajen kasar Masar, kuma za a kammala aikin ran 16 ko 17 ga watan nan da muke ciki.
A wannan rana kuma, shugaban hukumar yin bincike kan harkokin kasa ta Masar ya ba da umurnin rike kudade da kadarori na wasu shugabannin jam'iyyar 'yan uwa ta Musulmi da ke birnin Giza da sauran wuraren kusa da hedkwatar kungiyar da ke birnin Alkahira, daga cikin su har da shugaba da kuma mataimakin shugaba na hukumar gudanarwar ta jam'iyyar, Mohammed Badie da kuma Khairat El-Shater, shugaba da kuma manyan jami'an jam'iyyar neman yancin kai da adalci na jam'iyyar. A sa'i daya kuma, hukumar yin bincike ta kuma tsawaita lokicin tsare tsohon shugaban hukumar ba da jagora ga jam'iyyar da kwanaki 4 da zummar kara masa bincike kan laifinsa na ''zargin tsarin shari'a na kasar''.
A wannan rana da safe, hukumar gudanar da bincike kan harkokin kasa ta Masar ta sanar da fara yin bincike kan Mohamed Morsy wanda rundunar sojan kasa ta tumbuke shi daga mukamin shugaban kasa bisa laififfuka na aikace-aikacen leken asiri, hura wutar hare-hare da janyo tabarbarewar tattalin arzikin kasa. Amma kakakin jam'iyyar 'yan uwa ta Musulmi Jihad Haddad ya yi watsi da karar da ake wa Mohamed Morsy, tare da bayyana cewa rundunar sojojin kasar Masar take da alhakin tashe tashen hankalin dake faruwa a halin yanzu a kasar Masar. (Maryam)