Al-Beblawi ya yi wannan tsokaci ne yayin tattaunawarsa ta farko da gida talabijin mallakar gwamnatin kasar. A cewarsa yanzu haka kasar Masar na tsaka da wani irin yaki na farfado da tattalin arzikinta, da kuma maido da kyakkyawan yanayin tsaro. Bugu da kari Beblawi ya ce, an gudanar da dukkanin nade-naden mukaman da aka yi cikin sabuwar gwamnatin kasar ta rikon kwarya ne bisa cancanta da kuma lura da kwarewar jami'an.
Wannan dai kalamai na Firaministan rikon kwaryar na zuwa ne daidai lokacin da magoya bayan hambararren shugaban kasar Morsi, ke ci gaba da zaman dirshan, tare da gudanar da zanga-zangar kin amincewa da sauke zababben shugaban, ta hanyar abin da suka kira haramtaccen juyin mulkin soji.(Saminu)