Bisa rahoton ayyukan gwamnati da aka gabatarwa taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin a yau Talata 5 ga wata, yawan farashin kayayykin da Sinawa za su saya zai karu da kimanin kashi 3.5 bisa dari a wannan shekarar da muke ciki.
Kafin fara wannan taro shugaban hukumar kididdiga ta kasar Sin Ma Jiantang, ya yi hira da manema labaru, inda ya bayyana cewa, Sin za ta tabbatar da farashin kayayyaki a wannan shekara yadda ya kamata, a sa'i daya kuma, ya nuna cewa, Sin za ta ci gaba da samun bunkasuwar tattalin arziki kamar yadda aka gani a karshen watanni 3 na shekarar bara.
A ganinsa, akwai fannoni biyu da za su kawo tasiri ga farashin kayayyaki a shekarar 2013 a kasar Sin, wato hauhawar farashin kaya masu alaka da raguwar darajar kudi daga kasashen waje, da kuma manufofin da kasashe masu wadata suka dauka, na nuna sassauci a fannin tattalin arziki.
Duk da wannan hasashe, Sin na da karfi wajen tabbatar da farashin kayayyaki bisa sharadin samun girbi mai armashi a cikin 'yan shekaru da suka wuce a jere, da yawan kayayyakin masana'antu da aka samar wanda ya haura bukata, da kuma manufar kudi mai inganci da dai sauransu.
A cikin wannan shekara da muke ciki, burin da aka saka wajen samun karuwar GDP zai kai kashi 7.5 bisa dari. Game da batun saurin karuwar tattalin arziki, Ma Jiantang ya nuna cewa, a bara an taba fuskantar koma bayan saurin karuwar tattalin arziki, amma a wannan shekara Sin za ta yi kokarin tabbatar da samun bunkasuwar tattalin arziki kamar yadda aka yi a karshen watanni uku na shekarar ta bara.
Daga nan sai ya jaddada cewa, abin da aka sa a gaba wajen bunkasa tattalin arzikin kasar Sin shi ne, kara saurin juya hanyar raya tattalin arziki, musamman ma yiwa tsarin kwaskwarima, da kuma tabbatar da inganci da bunkasar tattalin arzikin. (Amina)