Kudaden da aka bayar a ranar Laraba ya kawo adadin kudade da aka sake zuwa dalar Amurka miliyan 446.93.
Da yake amsa tambayoyi daga Xinhua, darektan harkokin sadarwa na kamfanin iskar gas na kasar Ghana Guure Brown,Guure ya baiyana cewa ana biyan 'yan kwangila da kuma kamfanin SINOPEC ne bayan an karbi kudi daga rancen da bankin CDB ya bayar.
Kamfanin man fetur na kasar Sin (SINOPEC Group) wani babban kamfani ne na albarkatun man fetur da aka kafa a shekarar 1998 a madadin tsohon hukumar man fetur ta kasar Sin. (Lami Ali)