in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya gana da shugaban Nijeriya
2013-07-11 20:04:48 cri
A yammacin ranar Alhamis 11 ga wata, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Zhang Dejiang ya gana da shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan a birnin Beijing,fadar gwamnatin kasar.

A lokacin ganawar Zhang Dejiang ya bayyana cewa, majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta dora muhimmanci sosai kan bunkasa dangantaka tsakaninta da majalisar dokokin kasar Nijeriya. Tana fatan kara karfafa hadin gwiwa da sada zumunci da majalisar dokoki da ta wakilai na Nijeriya, a kokarin tabbatar da sakamakon da shugabannin kasashen biyu suka samu bisa majalisun, da zurfafa mu'amalar fasahohi, da sa kaimi ga karfafa hadin gwiwa a fannonin siyasa, tattalin arziki, cinikayya da sauransu tsakanin kasashen biyu, ta yadda za a zuba sabon kuzari wajen bunkasa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Nijeriya.

A nasa bangare, Shugaba Goodluck Jonathan ya ce, Nijeriya na fatan sa kaimi ga bunkasa dangantaka tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon mataki, da zurfafa mu'amala da hadin gwiwa tsakanin majalisun, a kokarin kawo alheri ga kasashen biyu da jama'arsu.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China