130711-Kara-zurfafa-dangantakar-abokantaka-tsakanin-Sin-da-Nijeriya-za-ta-taimaka-wajen-bunkasa-dangantaka-tsakanin-Sin-da-Afirka-inji-Goodluck-Jonathan-Bello
|
A ranar Alhamis 11 ga wata, shugaban kasar Nijeriya Goodluck Jonathan ya yi hira da wakilinmu inda yace ci gaba da zurfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Nijeriya, ba ma kawai za ta taimaka wajen bunkasa dangantaka tsakanin kasashen biyu ba, har ma za ta taimaka wajen bunkasa dangantaka tsakanin Sin da kasashen Afirka baki daya.
Shugaba Jonathan ya yi bayanin cewa, bisa dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, Sin ta ba da agaji ga kasashen Afirka da dama cikin yakini, hakan ya sa kaimi ga kasashen Afirka wajen samun ci gaba bisa kokarin kansu. A matsayin kasa mafi girma dake nahiyar Afirka, kuma kasa ta biyu a fannin bunkasa tattalin arziki a nahiyar, haka ma kasar da za ta dauki nauyin gudanar da taron kasashen Afirka na dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya na shekarar 2014, Nijeriya za ta kara zurfafa hadin gwiwa tsakaninta da masu zuba jari na Sin, da zurfafa mu'amala a fannin tattalin arziki da cinikayya, a kokarin kara hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu, kuma za ta yi kokarin kafa wani dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, da zummar sa kaimi ga bunkasa dangantaka tsakanin Sin da kasashen Afirka zuwa wani sabon mataki.(Fatima)