Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya ce, kamata ya yi kasa da kasa su girmama jama'ar kasashen Afirka wajen kyale su da su daidaita matsaloli da kansu, kuma su kara ba da hakikanin agaji ga kasashen Afirka domin samun ci gaba.
Mr Li wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis din nan 11 ga wata a lokacin da ya gana da Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan a Beijing, yana mai cewa, a fannin daidaita manyan batutuwa na shiyya-shiyya, kamata ya yi wadannan kasashen na duniya su sa kaimi ga kasashen Afirka wajen daidaita batutuwa ta hanyar yin shawarwari, a kokarin taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da neman samun ci gaba a nahiyar Afirka.
Ban da haka, Li ya kara da cewa, shawarwarin da shugabannin kasashen biyu suka yi a ranar Laraba 10 ga wata ya samu sakamako mai kyau, don haka Sin na fatan kara samun amincewa da juna a siyasance, da karfafa hadin gwiwa a duk fannoni tare da kasar Nijeriya, da kara mu'amala da ita kan harkokin duniya da na shiyya-shiyya, a kokarin sa kaimi ga kara bunkasa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata.
A nasa bangare, Shugaba Goodluck Jonathan ya bayyana cewa, Nijeriya ta yaba bisa ga muhimmiyar rawar da Sin take takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da neman samun bunkasuwa a duniya.
Nijeriya, in ji shi, tana godiya ga Sin wajen taimako da nuna goyon baya ga kasashen Afirka.
Goodluck Jonathan ya nuna fatan kara yin mu'amala da hadin gwiwa tsakanin kasarsa da Sin, a kokarin sa kaimi ga ciyar da dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma dangantaka tsakanin kasashen Afirka da Sin zuwa wani sabon mataki.(Fatima)