in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya koma gida bayan ya kammala ziyararsa a kasar Sin
2013-07-12 18:42:54 cri

Yau Jumma'a 12 ga wata da safe, shugaban kasar Nijeriya Goodluck Jonathan ya tashi daga birnin Beijing bayan da ya kammala ziyarar aikinsa a kasar Sin.

A cikin ziyarar ta yini 4 da shugaban kasar Nijeriya Goodluck Jonathan ya yi a kasar Sin, ya gana da takwaransa na kasar Xi Jinping, inda bangarorin biyu suka tsaida kuduri cewa, za a kara karfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu, da sada zumunta, da zurfafa hadin gwiwa irinta moriyar juna, da kara nuna goyon baya ga juna, a kokarin samun ci gaba tare da kawo alheri ga jama'ar kasashen biyu. Haka kuma, shi shugaba Jonathan ya gana da firaministan kasar Sin Li Keqiang da shugaban majalisar wakilan kasar Sin Zhang Dejiang bisa alkiblar raya dangantakar kasashen biyu.

Ban da harkokin siyasa ma, shugaba Jonathan ya yi shawarwari da shugabannin manyan kamfanonin kasar Sin da dama da suka yi aiki a kasar Nijeriya, don neman hanyar da za a bi wajen ci gaba da kyautata dangantakar cinikayya da ke tsakanin kasashen Sin da Nijeriya ta fuskar tattalin arziki, tare da daddale yarjejeniyoyi da dama a tsakaninsu.

Haka kuma, Goodluck Jonathan ya halarci taron tattaunawar tattalin arziki da cinikayya, inda shi kansa da sauran shugabannin manyan kamfanonin kasar Sin suka yi kiraye-kiraye ga 'yan kasuwan kasar Sin da su kara zuba jari a kasar Nijeriya.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China