Yayin da taron manema labarai na taron farko na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa karo na sha biyu, Lin Yifu ya nuna cewa, gaskiya ne a halin yanzu, ba a samu kyakkyawan yanayin raya tattalin arzikin a duniya ba, amma yanayin tattalin arzikin kasar Sin na cikin yanayi mai kyau, shi ya sa, yana da imani cewa, cikin shakarar da muke ciki yanzu, nan da shekaru masu zuwa, Sin za ta ci gaba da samun bunkasuwa, tare da ciyar da ayyukan bunkasa birane gaba, da kuma dukufa wajen gudanar da ayyukan kiyaye muhalli, hakan ya sa, za a samar da karin damar zuba jari a kasar Sin.
Yayin da ya ke magana kan batun darajar musayar kudin Sin, Lin Yifu ya bayyana cewa, sabo da a halin yanzu, galibin darajar kudaden duniya na ci gaba da raguwa, wanda ya haddasa karuwar darajar kudin Sin, shi ya sa, ya kamata a canja manufar kudin kasar yadda ya kamata, bisa karfin kera hajoji a kasar da kuma yanayin cinikayyar ketare.
Lin Yifu ya kara da cewa, mai iyuwa ne, yawan kudin da aka samu wajen samar da kayayyaki zai ci gaba da samun karuwa da kashi 8 bisa dari cikin shekaru 20 masu zuwa. (Maryam)