A hirar da yayi da wakilinmu a nan Birnin Beijing,lokacin da ya kawo ziyarar aiki na kwanaki 4,Mr Jonathan yace harshen hausa ya zama kamar uwar harsuna a arewacin Nigeriya kuma daya daga cikin mayan harsuna 3 da ake amfani da su a kasar,don haka wannan kokari abin a jinjina ne kwarai saboda an samo wata hanyar sada zumunci.
Daya tabo maganar film din sinanci da aka fassara kuma ake shirin fara watsawa cikin harshen hausa a Nigeriya wanda musammam aka gayyato wassu 'yan wasan kwaikwayo daga Nigeriya suka zo suka dora murya akai yace wannan ba karamin dabara bace,domin yanzu haka a cikin yarjejeniyar da kasar sa ta sanya ma hannu da kasar Sin akwai na musanyar al'adu,wanda zai taimaka gaya ma al'ummomin kasashen biyu wajen fahintar juna.
Shugaba Jonathan ya kuma mika godiyar sa bisa ga wannan kokari na fassara film din sinanci zuwa harshen hausa tare da fatan nan gaba kuma za'a yi kokarin fassara makamancin fina finan cikin sauran harsuna na Nigeriya har ma suma Kasar Sin zasu fassara wassu fina fina daga Nigeriya zuwa Sinanci,domin Sinawa su kalla su kara fahimtar al'adun mutanen Nigeriya. (Fatimah Jibril)