Shugaban kwamitin shawarwari da hada kan 'yan kasa na Mali (CDR), Mohamed Salia Sokona a karkashin wata tawagar CDR zai fara wani rangadi daga ranar 9 zuwa 11 ga watan Yuli domin wayar da kan jama'a da fadakarwa tare da yin musanya tare da al'ummomin dake yankunan kasar Mali, zai fara zangon farko ranar Talata a yankin Kidal, a wani labari na ranar Litinin.
A yayin wannan rangadi, mambobin CDR da shugabansu za su kai ziyarce-ziyarcen sada zumumci da gudanar da taruruka a yankunan Kidal, Sikasso, Gao, Kayes, Mopti, Segou, Tombouctou da Koulikoro.
Tun bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar ranar 18 ga watan Yunin da ya gabata a Ouagadougou tsakanin gwamnatin kasar Mali da gungun kungiyoyin 'yan tawayen MNLA da kuma babban kwamitin hadewar yankin Azawad (HCUA), babban aikin ya dawo ga kwamitin CDR ta fuskar sasanta 'yan kasar Mali baki daya.
Dalilin haka ne manzon musammun na shugaban kasar Mali da aka dora wa nauyin tattaunawa tare da kungiyoyin 'yan tawayen arewacin Mali, mista Tiebile Drame ya sheda wa manema labarai bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar cewa, 'Kwamitin CDR zai fara aikinsa ba tare da bata lokaci ba, na yi imanin cewa, kafa hanyoyin sasanta 'yan kasar Mali zai kawo cigaba da karfafa kasarmu maimakon gurguntar da ita'. (Maman Ada)