Dakaru dake rajin 'yantar da yankin Azawad a arewacin kasar Mali, karkashin inuwar kungiyar MNLA, da HCA, da kuma kungiyar masu kishin Islama ta MIA, sun fara rushe sansanin sojin kasar na biyu dake arewacin Kidal.
Rahotannin da kamfanin dillancin labaru na kasar Sin Xinhua ya samu daga yankin sun bayyana cewa, sansanin wanda aka gina a shekarar 1997, dake da nisan mita 2,500 daga gabashin karamin filin sauka da tashin jirage dake Kidal, na taimakawa wajen tabbatar da tsaron kasar ta Mali.
Rushe wannan sansani dai ya biyo bayan wata kwarya-kwaryar yarjejeniya ce da aka daddale a birnin Ouagadougou, na kasar Burkina Faso, tsakanin bangaren mahukuntan kasar, da kuma tsagin kungiyar ta MNLA, da kuma majalissar zartaswar kungiyar hadin kan yankin na Azawad, ko HCUA a takaice, a ranar 18 ga watan Yunin da ya gabata, yarjejeniyar da ta tanaji gudanar da babban zaben kasar ranar 28 ga watan Yulin nan, tare da share fagen hawa teburin shawara don warware daukacin matsalolin kasar.
Idan dai ba a manta ba, cikin watan Maris na shekarar 2012 ne, MNLA ta kame yankin arewacin kasar, biyowa bayan juyin mulkin da ya auku, ta kuma bayyana ballewar wannan yanki, ko da yake dai hakan bai samu karbuwa daga bangaren kasashen duniya ba. A kuma farkon shekarar nan ta 2013, sojojin kasar ta Mali, da hadin gwiwar dakarun kasar Faransa, da na ragowar kasashen Afirka suka fafata da 'yan tawayen kasar dake rike da ikon yankin arewacin kasar, kafin daga bisani kungiyar ta MNLA ta amince da batun warware takaddamar dake wakana ta hanyar siyasa, karkashin zaman da kasar Burkina Faso, a madadin kungiyar ECOWAS ta jagoranta. (Saminu)