in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a gudanar da babban zaben shugaban kasa a Mali bisa lokacin da aka tsara
2013-07-11 17:11:23 cri
Bisa labarin da aka samu daga kafofin watsa labarai na kasar Mali a ranar 10 ga wata, an ce, shugaban wucin gadi na kasar Mali Dioncounda Traore ya bayyana a Bamako, babban birnin kasa cewa, bisa jadawalin da aka tsara, za a kada kuri’un babban zaben shugaban kasa zagaye na daya ran 28 ga watan Yuli Kuma ran 9 ga wata, Mr. Traore ya gana da ‘yan takara guda 28 da za su shiga babban zaben a fadar shugaban kasa, inda ya bayyana cewa, koda yake an riga an kawo karshen rikice-rikice dake addabar kasar, a hannu guda, kawo wannan lokaci ba a samu cikakken yanayin kwanciyar hankali a kasa ba, shi ya sa babban aikin dake gaban sabon shugaban kasa shi ne, warware matsalolin da kasar ke gamuwa da su a halin yanzu, da kuma samar da damar ciyar da kasar gaba. Traore ya kara da cewa, ko da yake wasu daga ‘yan takarar na fatan a jinkirta babban zaben, sai dai wannan dabara ba za ta iya warware matsalolin da kasar ke fama da su a halin yanzu ba, muddin dai gwamnatin wucin gadi, da ‘yan takarar ba su hada kai wajen warware matsalolin ba. Dukkan ‘yan takara suna zaman daidai wa daida kafin zaben. (Maryam)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China