in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wata kungiyar addinin Islama ta dauki niyyar mara wa wani 'dan takarar zaben shugaban Mali
2013-07-03 10:58:55 cri

Wata kungiyar addinin Islama da ake lakabin SABATI dake kunshe da gungun kungiyoyin addinin Islama ta bayyana niyyarta na kawo goyon baya ga wani 'dan takarar zaben shugaban kasa na ranar 28 ga watan Yuli a kasar Mali, in ji Moussa Boubacar Bah shugaban SABATI a ranar Talata a birnin Bamako a yayin wani taron manema labarai. 'Mun dauki niyyar mara wa wani 'dan takarar zaben shugaban kasa na ranar 28 ga watan Yuli mai zuwa, babu wani muhimmanci da ya kasance musulmi, kirista ko wanda ba yada addini. Abin da muke fata shi ne ya samu karfin bunkasa kasar Mali, kasar dake da mabiya addinai daban daban. Ta wannan niyya, muna fatan kawo namu taimako wajen fadada tsarin demokaradiyar kasar Mali.' in ji mista Bah.

Amma a cikin watan Mayun da ya gabata, bayan wani babban taron kwamitin addinin Islama na kasar Mali (HCI), shugaban wannan hukuma ta addinin musuluncin kasar Mali, Iman Mahmoud Dicko, tare da makarrabansa sun ba da sanarwar cewa, kwamitin HCI ba zai goyi bayan kowane 'dan takarar zaben shugaban kasa ba, matakin da ya samu amincewa daga shugabannin jam'iyyun siyasar kasar Mali kamar tsohon faraministan kasar Zoumana Sako na jam'iyyar CNAS. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China