Ma'aikatar harkokin waje ta kasar Somaliya a cikin wata wasika da ta mikawa kungiyar AU da tawagar musamman ta AU dake Somaliya ta yi bayanin cewa, saboda birnin Kismayo dake dab da teku na shan fama da rikicin siyasa, wasu shugabannin tawaga ta musamman na AU ba su iya ayyukan su, hakan ya sa gwamnatin kasar ta yi kira ga AU da ta tura karin sojojin sauran kasashe zuwa wannan wuri tun da wuri.
Gwamnatin kasar ta shaida cewa, yawan mutanen da suka mutu cikin hargitsi tsakanin kabilu daban-daban a birnin Kismayo ya kai 65, yayin da wasu fiye da 150 suka ji rauni. Gwamnatin na yi shirin kafa wata hukumar gudanarwa birnin Kismayo, don kula da kudancin kasar amma wasu kabilu sun yi hadin kai da sojojin Kenya domin kafa wata jihar mai zaman kanta, hakan ya sa gwamnatin ba ta yarda ba.
Har ila yau gwamnatin Somaliya ta yi kira ga AU da ta yi bincike kan wannan lamari nan take, tare kuma da neman rundunar kasar Kenya da ta saki hafsoshin sojojin gwamnatin Somaliya da ta tsare.
Wakilin musamman na AU dake Somaliya Mahamat Saleh Annadif ya bayyana a wannan rana cewa, AU na fatan yin hadin kai da gwamnatin Somaliya domin kwantar da halin da ake ciki a yankin Kismayo, inda aka yi kokarin jawo baraka. (Amina)