Wata sanarwa daga ofishin kakakin magatakardar MDD, ta bayyana nadin babban ministan a ofishin fadar shugaban kasar Senegal mai suna Abdoulaye Bathily, a matsayin sabon mataimaki na musamman ga magatakardar MDD, kan shirin wanzar da zaman lafiya da samar da daidaito a kasar Mali, shirin da akewa lakabi da MINUSMA.
An bayyana nadin na Bathily ne tare da takwaransa daga kasar Amurka David Gressly, wanda shi ma zai yi aiki karkashin ofishin tawagar ta MINUSMA, a matsayin mataimaki na musamman ga magatakardar MDD. Har ila yau, Gressly zai kasance jami'in tsare-tsare na MDD mai lura da ayyukan jin kai, kuma wakilin shirin MDD na samar da da ci gaba karkashin hukumar UNDP.
Idan dai za a iya tunawa a cikin watan Afirilun da ya gabata ne dai kwamitin tsaron MDD, ya amince da tura dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD 12,600 zuwa kasar ta Mali, da zummar karbar aiki daga tawagar AFISMA da kasashen nahiyar Afirka ke jagoranta. Yayin da kuma a hannu guda aka dorawa rundunar MINUSMA nauyin taimakawa shirin warware matsalolin siyasa dake addabar kasar ta Mali, kasar da ke shan fama da rikici-rikice tsakanin dakarun gwamnati, da na 'yan tawayen Azbinawa tun daga farkon shekarar bara, lamarin da ya haddasa tserewar dubban al'ummarta daga gidajensu. (Saminu)