Daraktan gudanarwa a ofishin hukumar ayyukan tsarawa da gudanar da ayyukan jin kai ta MDD, ko OCHA a takaice, John Ging, ya bayyana bukatar kara yawan tallafi da ake samarwa, domin gudanar da ayyukan jin kai da raya ci gaban al'umma a Somalia, matakin da a cewarsa zai magance yaduwar rikici dake addabar kasar yanzu haka.
Ging ya yi wannan kira ne cikin wata sanarwa da aka rabawa manema lanbarai ranar Asabar 13 ga wata, bayan kammala wata ziyarar aiki da ya kai kasashen Kenya da Somalia, Daraktan ya ce ya zama wajibi yayi kira ga kasashen duniya, da su samar da tsarin da zai tallafi wannan kasa da rikice-rikice suka addaba tsahon lokaci.
Daga nan sai sanarwar ta bayyana irin rashin jin dadin babban jami'in hukumar ta OCHA, don gane da harin da aka kaiwa ginin ofishin MDD ranar 19 ga watan Yunin da ya gabata a birnin Mogadishu, yana mai jajantawa iyalai da al'ummar kasar bisa faruwar wannan lamari. Ging ya ce, ba za a taba mantawa da gudummawar da wadannan ma'aikata suka baiwa aikin jin kai ga al'ummar kasar ta Somaliya ba. Cikin wadanda suka rasa rayukansu a yayin harin akwai jami'in kasar waje guda daya, da wasu 'yan kwangila 3, da kuma wasu masu gadi 'yan Somaliya su 4. An ce harin ya kuma sabbaba mutuwar wasu karin mutane dake wajen ginin, tare da jikkata wasu da dama.
Kididdigar da hukumar ta OCHA ta fitar dai na nuna cewa, kimanin mutane miliyan guda ne a kasar ta Somaliya ke da bukatar tallafin gaggawa, yayin da kuma wasu karin mutanen kimanin miliyan 1.7 ke bukatar tallafin kandagarki ga barin sake afkawa cikin halin ni-'ya su. Har wa yau akwai dubban yara kanana da ba sa iya samun abinci mai gina jiki, baya ga cutar shan inna da rahoton yace ta sake bulla a kasar, bayan bacewarta tsahon shekaru 6 da suka gabata.(Saminu)