Shugaban wucin gadi na kasar Mali Dioncounda Traore ya gana a ranar Talata da yamma a fadar shugaban kasa ta Koulouba tare da 'yan takara 28 na zaben shugaban kasar da kotun kolin kasar ta amince da su domin tattaunawa bisa zaben shugaban kasa da zagayen farko da za'a gudana a ranar 28 ga watan Yulin da muke ciki.
An yi ganawar a gaban firaministan kasar Django Cissoko da ministan dake kula da hukumomin kasa da fasalin kasa Kanal Moussa Sinko Coulibaly.
Tattaunawar da aka yi ta zo kwanaki biyu bayan bude yakin neman zaben shugaban kasa zagayen farko, kuma ta kasance wata babbar dama ga shugaba Diocounda Traore da illahirin wadannan 'yan takara na yin shawarwari, ta yadda kowane daga cikinsu zai gane nauyin dake bisa wuyansa domin ganin an cimma nasarar wannan zabe.
Shugaban kasar Mali ya jinjinawa 'yar takara mace guda, madam Haidara Aissata Cisse dake bayyana niyyar matan kasar Mali na neman damar shiga cikin harkokin cigaban kasarsu. Hakazalika mista Traore ya tunatar da 'yan takarar da wakilansu cewa, bayan wannan zabe, dan takara guda ne zai ci nasara, don haka ya zama wajibi sauran 'yan takara su amince da sakamakon zabe. (Maman Ada)