A ranar Lahadi, aka kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa zagaye na farko a dukkan fadin kasar Mali. Yayin yakin neman zabe na tsawon makwanni uku, dukkan 'yan takara da kotun kolin kasar ta tabbatar da sunayensu, sun gabatarwa al'ummar kasar baki daya jadawalin ayyukansu na yi wa talakawa aiki da bautawa kasa. Tun ranar Lahadi da safe a Bamako, bayan da aka bude wannan kamfe, a ko ina fotunan 'yan takara ne kamar su Soumaila Cisse na jam'iyyar URD, Modibo Sidibe na gungun jam'iyyun FARE, Mountaga Tall na jam'iyyar CNID, Soumana Sako na jama'iyyar CNAS. Haka kuma abin da za'a yi la'akari shi ne matsayin da 'yan takara suka dora kan yawancin jihohin da suka zaba domin bude yakin neman zabe. Misalin dan takara Dramane Dembele na jam'iyyar ADEMA mafi girma a kasar Mali da kuma Cheick Boucadary na jam'iyyar PASJ, dan tsohon shugaban kasar Mali Moussa Traore kuma dan takarar jam'iyyar CARE. Haka kuma Soumaila Cisse, tsohon shugaban kwamitin kungiyar UEMOA dan takarar jam'iyyar URD shi ma ya bude yakin neman zabensa tun daga yankin Mopti na kasar Mali.
Kafin kaddamar da wannan kamfe, dokta Mamadou Diamoutani, shugaban kwamitin zabe mai zaman kansa CENI, a cikin jawabinsa tanyar kafofin gwamnati ya yi kira ga dukkan 'yan takarar 28 da su girmama dokokin zabe yadda ya kamata domin kauce wa duk wani rikici a tsawon wannan lokaci. (Maman Ada)