Kwanan baya, a wajen taron gabatar da rahotanin aiki ga kafofin yada labaru na gwamnatin kasar na dandalin ministoci na shekarar 2013 na Nijeriya da aka shirya a birnin Abuja hedkwatar kasar, ministoci da wakilan hukumomi da dama sun ba da jawabi, ciki hadda ministan al'adu, yawon shakatawa da ba da shawara ga ayyukan kasar. Mai ba da shawara ga jakadan kasar Sin dake Nijeriya Malam Jin Hongyue shi ma ya halarci taron a matsayin daya daga cikin wakilan 'ma'aikatan diplomasiyya na kasa da kasa.
A cikin jawabinsa, ministan al'adu, yawon shakatawa da ba da shawara ga ayyukan kasar Edem Duke ya yaba sosai ga ci gaban da kasashen Sin da Nijeriya suka samu dangane da yin mu'ammalar al'adu da hadin gwiwa tsakanin su a shekarun nan. Yana mai cewa, Nijeriya ta kasance kasar farko dake nahiyar Afrika da ta kafa cibiyar al'adunta a kasar Sin, kuma ta kaddamar da aikin yada al'adun Nijeriya wanda aka kwashe mako daya ana yin shi a ko wace shekara, Sin kuwa ta goyi bayan ayyukan da Nijeriya ta yi a wannan fanni, hakan ya mai da aikin yin musayar al'adu tsakanin kasashen biyu a wani sabon matsayi a tarihi, ganin yadda a karo na farko Sin ta fara shiga shagalin nuna al'adun Nijeriya a Abuja a shekarar bara, sa'anan a karo na farko da birnin Nanjing na kasar Sin ta kulla dangantakar hadin kai a fannin al'adu da Nijeriya, haka a karo na farko da Sin ta shiga bikin baje kolin kayayyakin fasaha na Afrika da ya gudana a Nijeriya a wannan shekara da muke ciki, hakazalika a karo na farko Nijeriya ta kaddamar da bikin nuna al'adun kasar a kasar Sin a shekarar bara, wanda ya gabatar da kide-kide da raye-raye na gargajiya na kasar ga jama'ar kasar Sin.
Dadin dadawa, mista Edem Duke ya bayyana cewa, yin musayar al'adu tsakanin kasashen biyu zai taimaka wajen kara fahimtar juna da kara dankon zumunci tsakanin jama'ar kasashen biyu. (Amina)