in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Jonathan na Najeriya yayi kira da a kara hada kai wajen yaki da ta'addanci
2013-06-19 16:20:18 cri
Shugaban tarayyar Najeriya Dr. Goodluck Ebele Jonathan yayi kira ga kasashen duniya, dasu kara hada kai wajen yaki da ayyukan ta'addanci a dukkanin sassan duniya.

Shugaba Jonathan yayi wannan kira ne a ranar Talata a birnin tarayya Abuja, lokacin da yake karbar takardun fara aikin sabbin jakadun da aka turo kasar Najeriya a fadar shugabansa dake Aso Rock, ciki har da sabbin jakadun Isra'ila, da Rasha, da Girka, da Aljeriya da kuma Senegal.

Jonathan ya ce, Najeriya da sauran kasashe za su ci gajiyar irin wannan hadin-gwiwa mai karfi da ake yi tsakanin hukumomin tsaronsu, a wani kokari na yaki da ayyukan ta'addanci a gida da waje. Ya gayawa sabbin jakadun cewa, Najeriya na maraba da karfafa hadin-gwiwa, tare da duk wata kasa wadda ke da kwarewa a fannin yaki da ta'addanci a cikin gida.

Jonathan ya kuma bayyanawa sabon jakadan kasar Isra'ila dake Najeriya Mista Uriel Palti cewa, yana sa ran kai ziyara kasar Isra'ila nan bada jimawa ba, inda zai tattauna da firaministan kasar Benjamin Netanyahu, dangane da shirin inganta hadin-gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Har wa yau kuma, shugaba Goodluck Jonathan ya bada tabbaci ga wadannan sabbin jakadu cewa, gwamnatin tarayyar Najeriya zata nuna musu cikakken goyon-baya, domin kara kyautata dangantakar abokantaka tsakanin Najeriya da wadannan kasashe.

Wadannan sabbin jakadu sun bayyana farin-cikinsu game da soma ayyuka a Najeriya, haka kuma sun sha alwashin cewa, za su nuna kwazo domin inganta alakar diflomasiyya, da tattalin arziki tsakanin kasashensu da Najeriya.

Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China