An yi bikin kaddamar da wata gada a birnin Ibadan hedkwatar jihar Oyo dake kudu maso yammacin kasar a ran 25 ga wata, da reshen Nijeriya na kamfanin kula da ayyukan gine-gine na kasar Sin ya ba da taimako wajen gina wa.
Gwamnan jihar Abiola Adeyemi Ajimobi ya ce, wannan gadar ketare titi ta kasance ta farko a jihar da ta hada hanyoyi daban-daban da dama, wadda ta sake shaida karfin kamfanin bayan ya shiga aikin ceto bayan abkuwar ambaliyar ruwa a jihar. Ya ce, wannan aiki zai taimaka wajen sassauta halin da ake ciki a kudu maso yammacin kasar na rashin kyan hanya, da kuma ba da taimako wajen gaggauta bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma a wannan yanki.
Manajan kamfanin Li Bing ya ce, kamfanin ya yi wannan aiki ne bisa iyakacin kokarinsa, wannan gada mai inganci ta nuna alamar kyan kamfanin a jihohi daban-daban da ke kudu maso yammacin kasar, har ma ta taka rawa wajen samar da guraben aikin yi da kyautata zaman rayuwar jama'ar wuri. (Amina)