Wannan gasar rubuta bayani da aka gudanar a watan Mayu na bana, ta samu karbuwa sosai a tsakanin bangarori daban daban, kuma an samu bayanai 188 na Sinanci ko Turanci a ciki wata guda. Game da wannan, Liu Xianfa ya bayyana cewa, an samu irin wannan nasara ne kasancewar gwamnatocin kasashen biyu sun dora muhimmanci kan raya dangantakar hadin gwiwarsu, kana kungiyoyi masu zaman kansu na kasashen biyu su ma sun yi hadin gwiwa sosai. Matakin da ya bayyana al'adun kasashen Sin da Nijeriya tare da karfafa zumunci mai zurfi a tsakanin jama'arsu.
Mai lambar yabo ta farko ta "labarina game da kasar Sin" kuma malama mai koyar da Sinanci a kwalejin Confucius ta jami'ar Lagos a tarayyar Nijeriya Victoria Arowolo ta bayyana a gun bikin cewa, ta bayyana kaunarta game da jama'a, harshe da kuma al'adun kasar Sin ta hanyar shiga gasar rubuta bayanin. Ta yi imani da cewa, a karkashin kokarin jama'ar kasashen biyu, za a kara samun ci gaba kan dangantakar abokantaka a tsakanin kasashen biyu. (Zainab)